20 Afirilu 2021 - 14:51
Dan Idriss Deby, Zai Shugabanci Chadi Na Tsawon Watanni 18

A Chadi, an kafa majalisar sojoji wacce dan Idriss Deby, Janar Mahamat Deby zai jagoranta domin shuganacin kasar har na tsawon watanni 18.

ABNA24 : Janar Mahamat Deby, shi ne babban kwamandan rundinar tsaron lafiyar shugaba Idriss Deby.

An kuma sanar da rusa majalisar dokoki da kuma ta ministoci.

Da safiyar yau Talata ne rundinar soijn Chadin, ta sanar da mutuwar shugaba Idriss Deby Itno, bayan raunin da ya samu a fagen daga a yaki da 'yan tawaye.

Idriss Deby, wanda shi ma tsohon dan tawaye ne ya kwaci mulki a shekarar 1990, bayan hambarar da gwamnatin Hissen Habre.

A baya baya nan ne dai 'yan tawayen FACT suna tunkari birnin N'Djamena.

342/